HANYOYIN DA ZA KI BI DOMIN MAGANCE BUSHEWAR GASHIN KAI “Kwalliya ba ta cika sai da kai gyararre. Duk irin jan baki da hodar da za ki shafa, da jagira da zizaren da za ki saka ko ki goga, in har gashin kanki ba a gyare yake ba, to, fa har yanzu da sauran kwalliya” ‘Yan uwana mata, ina me yi muku sallama irin ta addinin musulunci Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu A yau za mu yi duba ne kan hanyoyin warware wata matsala mai cin tuwo a kwaryarmu mu mata. Matsalace da za mu iya kira da karama kuma babbar matsala. Karamar matsala ce in har an san hanyar da za a maganceta, kuma babbar matsala ce in ba a san hanyar da za a bi wajen magancenta ba. Za mu tattauna ne a kan hanyoyin da zamu bi don magance matsalolin bushewar gashin kai. Mata da dama na fama da wannan matsalar, wasu da zaran sun ji kan su ya bushe, maimakon su fara hada kwabin gashin kai don magance wannan matsalar, sai kawai su dauko man gashi su shafe kansu da shi, wanda yin hakan na iya zama sanadiyar dankarewar gashi, toshe kofofin gashi da hana fitowarsa, musamman idan gashi ya dade ba’a wanke shi ba. Sannan hakan zai iya bawa amosanin kai damar fitowa. Hanyoyin da za ki bi domin magance bushewar gashin kai sune kamar haka: 1.Kwabin Ayaba Kayan hadi Zuma cokali daya, Nunanniyar Ayaba. Yadda ake hadawa Za ki bare bawon Ayaba sai ki markada a injin nika (blender) ta markadu sosai. Ki zuba zuma cokali daya ki gauraya su su hadu, sannan ki shafa a gashi tun daga karkashin sa har baki. Ki rufe kan da hular leda (shower cap). Bayan mintuna 15- 20 sai ki wanke kan da sabulun wanke gashi (Shampoo) da na karawa gashi maiko (conditioner). 2.Kwabin man Zaitun da man Kwakwa. Man zaitun Man kwakwa Yadda ake hadawa 1.Man zaitun za ki hada da Man kwakwa, sai shafa hadin tun daga karkashin gashi Ki tufke gashin waje daya, sannan ki sa hular leda Bayan mintuna 15-30 sai ki wanke da sabulun wanke gashi da na karawa gashi maiko Ga masu laushin gashi yana da kyau su yi amfani da na Ayaba, domin tana kunshe da sinadarin “ potassium” wanda ya ke taimakawa gashin kai wajen sa shi ya yi karfi, yayi kyau. Sannan yana da kyau don samun kyakkyawan sakamako, ki yi kamar sau biyu a sati. Allah yasa mu dace. Yadda Za Ki Kula Da Gashinki Kowane Irin gashi ke gareki yana bukatar wankewa akai-akai da sabulun wankin gashi wanda ya dace da irin gashin da kike dashi (za a ga bayanin haka a rubuce a jikin sabulun) Duk da cewa mata ba su fiye son wanke gashinsu ba saboda gudun kada ya kankance, amma akwai bukatar akalla a wanke shi sau daya a cikin makonni biyu. Tun kafin a wanke gashin, idan akwai amosani, ya kamata a kankare shi, don kada sai an wanke ya rika tasowa yana bata gashin. Sannan akwai bukatar a nemi maganin amosani na musamman. Bayan wanke gashi sai a bar shi ya bushe, ba a son taje jikakken gashi, sannan sai a shafa masa mai wanda ya yi dai dai da gashin. Idan kitso kika fi so, bayan kin wanke kin shafa masa mai sai ki rangada wanda kike so. Sai dai kuma kada ki bar kitson ya wuce makonni biyu ba tare da kin kwance ba. Idan kuwa baki son kitso, a kullum dole ne ki zauna ki taje gashin tare da shafa masa mai, sannan sai ki daure shi da madaurin gashi (Ribbon) dai dai yadda kike so. Idan da hali, Zai yi kyau duk bayan wata daya kije salun ki yi masa abin da ake kira steaming, wannan ne zai hana shi karkadewa. Idan kuma ke mai sha’awar yi wa gashi shamfo ce (retourching) shi ma akwai bukatar ki rika maimaitawa a duk bayan watanni biyu. Idan kuma gashinki mai karfi ne za ki rika yi kamar sau daya a wata.Yawan yin shamfo a cikin kwanakin da suka gaza wata guda, masana sun ce akwai yiwuwar zubewar gashi saboda yawan kone shi da ake yi. Bayan duk kin gama wadannan akwai turaren gashi da za ki rika feshe gashin ki da shi, don ya rika sa shi kamshi na musamman kuma ya kamata ki sani cewa mayukan da ya yi wa wata aiki ba lalle ya yi miki ba, don haka ki kula sosai wajen zabar wanda zai dace da naki gashin. . Yam mata ahuta da acuci maza. . Domin neman karin bayani ko tambaya, shawara ko gaisuwa mu hadu a WHATSAPP ko FACEBOOK. . ππ FACEBOOK- ahmed bello sardauna
Monday, July 6, 2020
Karanta hanyoyinda zakibi domin gyara gashinki a saukake, anan ππ π
Tags
About sardauna novels
sardauna Novels Is 24 hours online books and Updates blog that share latest Nigerian hausa writers, and also English novels, gyaran jiki ga diya mace, gyaran nono, maganin sanyi Infection, man gashi and lots more
Subscribe to:
Post Comments (Atom)


No comments:
Post a Comment